in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Afirka ta Kudu ya cimma nasara kan zargin da aka yi masa kan batun yanke kauna ga mulkinsa
2017-08-11 11:31:56 cri

A ranar 9 ga wata, jam'iyyar adawa ta kasar Afirka ta Kudu ta bukaci a rusa majalisar dokokin kasar da gudanar da zaben shugaban kasar kafin lokacin da aka tsara. Kafin hakan, shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma ya cimma nasara kan zargin da aka yi masa kan batun yanke kauna ga mulkinsa. Manazarta sun yi tsammani cewa, wannan ya shaida cewa, jam'iyyar ANC ta Zuma ta kiyaye nuna goyon bayansa, amma watakila rikicin dake tsakanin jam'iyyar adawa da jam'iyyar dake kan karagar mulkin kasar zai kawo rashin tabbaci ga yanayin siyasa na kasar.

A ranar 8 ga wata, an jefa kuri'u kan batun yanke kauna ga mulkin shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma a majalisar dokokin kasar. Domin yawan mambobin majalisar dokokin kasar da suka amince da batun bai kai rabin yawansu a majalisar ba, ba a zartas da batun ba. Wannan ne karo na 8 da shugaba Zuma ya cimma nasara kan batun yanke kauna ga mulkinsa bayan da ya hau kan kujerar shugabancin kasar.

Yawan mambobin majalisar dokokin kasar ya kai 400, guda 249 daga cikinsu su 'yan jam'iyyar ANC dake kan karagar mulkin kasar. Bisa sakamakon da shugabar majalisar dokokin jama'ar kasar Baleka Mbete ta sanar, mambobin majalisar 384 sun jefa kuri'un, a cikinsu guda 198 sun jefa kuri'un kin amincewa, guda 177 sun jefa kuri'un amincewa, kuma guda 9 sun kaurace jefa kuri'ar.

Bayan da shugaba Zuma ya canja ministocin kasar a karshen watan Maris na bana, jam'iyyar adawa ta sake gabatar da batun yanke kauna ga mulkinsa.

Dalilin da ya sa hakan shi ne aka nuna shakka ga nada sabon ministan kudi da shugaba Zuma ya yi. Jam'iyyar adawa ta zargi shugaba Zuma da yin matsin lamba ga tsohon ministan kudi na kasar Pravin Gordhan lamarin da ya tilasta shi yin murabus, tun da cewa yana gudanar da aiki mai kyau da ake bukata, hakan ya kawo illa ga kasuwar hada-hadar kudin kasar.

Kana a ganin jam'iyyar adawa ta kasar, jam'iyyar ANC da shugaba Zuma ba su sa kaimi ga kasar Afirka ta Kudu wajen samun bunkasuwar tattalin arzikin kasar ba, kana ta zargi Zuma da iyalansa da aikata laifin cin hanci.

Jam'iyyar ANC ta ce, ana fuskantar matsaloli a kasar Afirka ta Kudu, amma ba a kyale nasarorin da kasar ta samu a karkashin jagorancin jam'iyyar ANC ba.

Manazarta sun yi tsammanin cewa, cimma nasara kan batun yanke kauna ga mulkin shugaba Zuma ya magance rikicin siyasa a kasar, yana da babbar ma'ana.

Bisa dokokin kasar, idan aka zartas da kuri'ar debe kauna ga shugaba Zuma, shugaban da dukkan majalisar ministocin gwamnatinsa za su yi murabus, kana Mbete za ta zama shugabar kasar ta wucin gadi. Daga baya, majalisar dokokin kasar ta zabi sabon shugaban kasar daga mambobin majalisar da ya maye gurbin Zuma a cikin wata daya. Idan ba a zabe shi ba, Mbete za ta rusa majalisar dokokin kasar, da gudanar da zaben shugaban kasar a cikin kwanaki 90.

Farfesa Richard na jami'ar Cape Town ta kasar Afirka ta Kudu ya yi nuni da cewa, yawancin mambobin majalisar dokokin kasar 'yan jam'iyyar ANC sun gano cewa, idan Zuma ya yi murabus, ba za su ji dadi ba. kana za a kawo rikicin siyasa a kasar Afirka ta Kudu, da kawo illa ga harkokin cikin gida da na harkokin waje, hakan zai kawo matsala mafi tsanani ga bunkasuwar tattalin arzikin kasar.

Ministan tsaron kasar Afirka ta Kudu Nosiviwe Mapisa-Nqakula ya bayyana a gun muhawara da aka gudanar a majalisar dokokin kasar cewa, muddin jam'iyyar adawa da take son Zuma ya yi murabus ita ce tube jam'iyyar ANC wadda ta zama jam'iyyar dake kan karagar mulkin kasar ta hanyar yin zabe, babu shakka aikin da jam'iyyar adawa ta yi a wannan karo shi ne aikin juyin mulkin kasar. Don haka, tilas ne mambobin majalisar dokokin kasar 'yan jam'iyyar ANC su hadi kai don murkushe yunkurin jam'iyyar adawa.

Wannan ne karo na farko da aka jefa kuri'u a asirce kan batun yanke kauna ga mulkin shugaban kasar, wanda ya shaida goyon bayan da mambobin majalisar dokokin kasar 'yan jam'iyyar ANC suka nuna wa shugaba Zuma ko a'a.

Wani mamban majalisar dokokin kasar dan jam'iyyar ANC da ba ya son a bayyana sunansa ba ya ce, a wannan karo, jam'iyyar ANC ta cimma nasara da kyar, ya yi kashedi ga shugaba Zuma da jam'iyyar ANC cewa, ya kamata a kara yin kokarin warware matsalolin yaki da cin hanci, bunkasuwar tattalin arziki, da rage yawan mutanen da ba su da aikin yi da matsalar karuwar yawan masu aikata laifuffuka da dai sauransu. (Zainab Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China