in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An cika shekaru 70 da kafuwar jihar Mongoliya ta gida na kasar Sin
2017-08-09 10:38:47 cri

A jiya Talata 8 ga wata ne aka yi bikin taya murnar cika shekaru 70 da kafuwar jihar Mongoliya ta gida mai cin gashin kan ta dake arewacin kasar Sin. Shugaban majalisar bada shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin Yu Zhengsheng, wanda ya jagoranci tawagar wakilan kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta Sin domin halartar bikin ya jaddada cewa, kafuwar jihar Mongoliya ta cikin gida ya zama kyakkyawan misali na gudanar da tsarin yankin kabila a kasar Sin, kana ana samun bunkasuwar tattalin arziki, da zamantakewar al'umma, da kyautata zaman rayuwar jama'a a yankin.

A gun bikin taya murnar cika shekaru 70 da kafuwar jihar Mongoliya ta gida mai cin gashin kanta na kasar Sin, wanda aka gudanar a ranar 8 ga wata, shugaban tawagar kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta Sin Yu Zhengsheng ya jaddada a cikin jawabinsa cewa,

"Kamata ya yi a bi hanyar da ta dace, a hade matakan dinkewar kasa da cin gashin kan jihar wuri guda, da hade kabilu da yankuna, da sa kaimi ga tsarin yankin kabilun kasar Sin wajen kara taka muhimmiyar rawa ta dinke dukkanin sassan kasar, da cikakken yankin kasar, da tabbatar da hadin kai da adalci ga kabilu, da samun bunkasuwa a yankunan kabilu, da kuma hada kan al'ummar kasar Sin gaba daya."

A halin yanzu, ana kiyaye bunkasuwar tattalin arziki a jihar Mongoliya ta gida mai cin gashin kanta cikin sauri, Yu Zhengsheng ya yi nuni da cewa,

"Kamata ya yi a kiyaye bunkasa tattalin arziki ba tare da gurbata yanayi ba, da sa kaimi ga yin tsimi da inganta makamashi, da samun bunkasuwa mai dorewa, da gudanar da manyan ayyukan yaki da kwararowar hamada, da kafa tsarin daji, da mayar da dazuka ta hanyar dakatar da ayyukan gona, da mayar da ciyayi ta hanyar dakatar da kiwon dabbobi, da tabbatar da kyakkyawan muhalli a yankin dake arewacin kasar Sin. Ya kamata a shigar da manufofin kasar Sin kamar 'ziri daya da hanya daya', da 'samun bunkasuwa tare na biranen Beijing da Tianjin da lardin Hebei', da gaggauta gudanar da tsarin bude kofa a dukkan fannoni, da sa kaimi ga bude kofa ga yankunan arewa da kasar Sin." (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China