A yayin shawarwari, Wang ya bayyana cewa, kasar Mongliya ta sake nanata matsayinta na martaba manufar Sin daya tak a duniya, tare kuma da girmama muradun Sin game da batutuwan da suka shafi yankin Tibet da dai sauransu, wannan na da ma'ana sosai ga bunkasa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. Wang ya kara da cewa, kasarsa na son bullo da wani shirin cudanya tsakanin manyan jami'an kasashen biyu, da karfafa hadin kai bisa manyan tsare-tsare, da ciyar da hadin kai a fannonin samar da kayayyaki, zuba jari da muhimman kayayyakin more rayuwa da dai sauransu. (Bilkisu)