in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD tana shirin kara yin amfani da yawan albarkatun ruwa a yankin kewayen gabar gabashin tekun Mediterranean da arewacin Afirka
2017-07-18 13:26:15 cri
Hukumar kula da abinci da aikin noma ta MDD ta sanar a birnin Alkahira dake kasar Masar a jiya cewa, za a dauki wasu matakai a yankin kewayen gabar gabashin tekun Mediterranean da arewacin Afirka don kara yawan albarkatun ruwa da ake yi amfani da shi.

Za a gudanar da wadannan matakai ne a kasashe 8 ciki har da Masar, Iran, Jordan da sauransu, kuma manufar wadannan matakai da ake fatan dauka shi ne taimakawa wadannan kasashe wajen cimma burin yin amfani da albarkatun ruwa da aka tsara a ajendar samun ci gaba mai dorewa ta MDD nan da shekatar 2030.

Wani jami'in MDD ya bayyana cewa, za a kara yawan albarkatun ruwa da ake yi amfani da shi ne don taimakawa kasashen dake yankin kewayen gabashin gabar tekun Mediterranean da arewacin Afirka, a wani makani na yaki da talauci, da tabbatar da tsaron abinci, da rage yawan marasa lafiya sakamakon rashin abinci da kuma inganta aikin samar da abinci. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China