in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD da Amurka sun yi tir da kisan dakarun kungiyar AU a Somalia
2017-08-01 10:34:05 cri
MDD da Amurka, sun yi tir da kisan jami'an wanzar da zaman lafiya 12 'yan asalin kasar Uganda da mayakan Al-Shabaab suka yi, yayin wani harin kwantar bauna a kudancin Somalia ranar Lahadi.

Cikin wasu sanarwoyi mabanbanta, Amurka da MDD sun ce ba kadai kan jami'an wanzar da zaman lafiya na AMISOM a kai wa harin na yankin Lower Shabelle ba, har ma da al'ummar da suke kokarin karewa.

Wakilin musamman na Sakatare-Janare na MDD Micheal Keating ya fada cikin sanarwar cewa, suna jinjinawa dakarun AMISOM da suka sadaukar da kansu wajen wanzar da zaman lafiya don samar da kyakkyawar makoma ga Somalia.

Har ila yau, ya ce yana kara jaddada goyon bayansu ga al'umma da gwamnatin Uganda, yayin da suke jimamin rashin 'yan kasarsu, inda kuma ya yi wa wadanda suka raunana yayin harin, fatan samun sauki.

Sanarwar da ofishin jakadancin Amurka dake Somalia ta fitar kuwa ta ce, Amurka na kara nanata aniyarta ta goyon bayan shirin AMISOM wanda ke aiki da gwamnatin Somalia don samar da kasa mai cike da tsaro da zaman lafiya da kuma ci gaba. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China