in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwajin jini ka iya gano hadarin samun karancin kwayoyin halitta cikin jini bayan an sha maganin cutar malaria
2017-07-06 10:19:33 cri

Wani rahoto ya bayyana cewa, za a iya yin gwajin jinin cutar zazzabin cizon sauro domin tantance ko marasa lafiya da suka sha maganin zazzabin na Artemisinin ka iya samun matsalar karancin kwayoyin hallitar cikin jini da ake kira Red Blood Cells.

Rahoton da mujallar Science Translational Medicine ta Amurka ta fitar a jiya, ya ce an yi kiyasin cewa, mutane biliyan 3.2 a kasashe 95 na cikin hadarin kamuwa da cutar malaria, kuma shan magunguna masu nasaba da artemisinins na kunshe da hadarin da ya kai kasa da kashi 5.

Sai dai, wasu marasa lafiya dake shan maganin za su iya shiga wani yanayi na karancin kwayoyin halitta na Red Blood Cells, makonni bayan an kashe kwayoyin cutar malaria.

A yanzu, babu wasu nagartattun hanyoyin gane marasa lafiya da za su iya shiga matsalar, wanda ke kashe kwayoyin halittar jinin wadanda suka sha maganin Artemisinin artesunate. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China