in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Afirka 47 sun amince da shirin kawar da zazzabin cizon sauro
2016-08-23 09:48:14 cri

Kasashen nahiyar Afirka 47 dake matsayin mambobi a hukumar lafiya ta duniya WHO, sun amince da wani kuduri na daukar matakan magance yaduwar cutar zazzabin cizon sauro ko malaria.

Kakakin babban magatakardar MDD Stephane Dujarric, shi ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai. Dujarric ya ce, kasashen sun amince da daukar wasu matakai na hakika, domin shawo kan wannan matsala.

Ya ce, duk da ci gaba da aka samu a fagen yaki da Malaria, wanda hakan ya rage kaso 66 bisa dari na mace mace dake faruwa sakamakon cutar daga shekara ta 2000 kawo yanzu, a hannu guda nahiyar ta Afirka na sahun gaba a fama da matsaloli masu alaka da wannan cuta. Ya zuwa bara, nahiyar Afirka ce ke da kaso 90 bisa dari, na daukacin al'ummun da wannan cuta ke hallakawa a dukkanin fadin duniya.

Alkaluman kididdiga sun nuna cewa, a bara kadai cutar Malaria ta kama mutane da yawansu ya kai miliyan 190, inda cikin su ta hallaka mutane 400,000. Kaza lika ya zuwa yanzu, al'ummar Afirka miliyan 800 ne ke cikin hadarin kamuwa da cutar.

Shirin ci gaban muradun karni na MDD ko SDGs, ya tanaji daukar karin matakan ganin bayan wannan cuta nan da shekara ta 2030, aikin da zai lakume kudi har dalar Amurka biliyan 66.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China