in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masana sun gano wani nau'in cutar malaria da ke halaka yara a Afirka
2015-03-19 09:51:26 cri

Wasu masana a kasar Amurka sun gano wani nau'in cutar malaria da ke kama lakar yara a nahiyar Afirka wadda daga bisani ke kai ga halaka su.

Madam Terrie Taylor ta jami'ar Michigan da ke kasar Amurka da tawagarta, sun bayyana a mujallar kimiyya ta New England cewa, an gano yadda kwakwalwar yaran da suka mutu sanadiyar wannan cuta ta malaria da ke kama laka ke kara girma sabanin wadanda suka mutu ba ta sanadin wannan cuta ba.

Masu binciken sun kuma gano cewa, kwakwalwar yaran da suka mutu sanadiyar wannan cuta na kumbura a lokacin da aka yi kokarin zaro ta daga cikin kokon kai sannan jijiyar da ke kula da nunfashi ita ma na motsewa. Lamarin da suka yi imanin cewa, shi ne ke sanya yaran mutuwa sakamakon rashin jan nunfashi.

Daga karshe bincike ya nuna cewa, kimanin kashi 65 cikin 100 na yaran da suka gamu da kumburin kwakwalwa na rayuwa. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China