in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta samu koma bayan hakar danyen mai mafi muni
2016-09-14 09:35:46 cri

Wasu alkaluma da kungiyar kasashe masu arzikin man fetur OPEC ta fitar na baya bayan nan sun nuna cewa, Najeriya ta samu koma baya wajen hakar danyen mai da bata taba fuskantar irinsa ba, lamarin da ya sa kasar ta sauka daga matsayinta na kasar Afrika mafi samar da danyen mai, inda kasar Angola ta karbi wannan matsayi.

Cikin rahoton cinikin mai na wata wata da aka fitar a ranar Litinin na watan Satumbar nan, OPEC ta bayyana cewa, kasashen Najeriya da Libya sun samu koma baya mafi muni wajen hakar albarkatun man.

Idan aka kwatanta da kasar Angola wacce a halin yanzu take iya hakar gangar danyen mai miliyan 1.782 a kowace rana, hako danyen man Najeriyar ya ragu zuwa ganga miliyan 1.677 a watan Maris.

Rahoton na OPEC ya kara da cewa, a watan Yuli, Najeriyar ta samu karuwar hako danyen man mafi girma, to sai dai duk da haka lamarin bai sa ta sha gaban Angola ba.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China