Babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin kuma shugaban kasar Sin kuma shugaban kwamitin rundunar soja ta kasar Sin Xi Jinping ya ba da muhimmin jawabi a gun taron taya murnar ranar cika shekaru 95 da kafa jam'iyyar kwaminis ta Sin a ranar 1 ga wata. Jaridar People's daily ta yi sharhi mai lakabin "Nacewa ga hanya irin ta kasar Sin da ci gaba da yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje."
Sharhin ya bayyana cewa, "ya kamata a nace ga yin imani kan hanyar zaman gurguzu musamman na kasar Sin da tsarin zaman al'umma da al'adu na kasar Sin da kuma manufofin JKS, domin ci gaba da raya zaman gurguzu iri na musamman na kasar Sin. A gun taron taya murnar ranar cika shekaru 95 da kafa jam'iyyar JKS, Xi Jinping ya nanata cewa, za a nace ga hanyar zaman gurguzu iri na musamman ta kasar Sin ba tare da kasala ba.
Ban da haka kuma, sharhin ya ce, a cikin shekaru 50 da suka gabata, yawan GDP ya ninka fiye da 200. A shekaru 30 da suka gabata, yawan mutanen birane da garuruwa na Sin ya karu da miliyan 500 ko fiye, matsakaicin tsawon rayukan jama'a ya fi na jama'ar kasashe masu ci gaba. Kana a cikin shekaru 10 da suka gabata, dukkan jama'ar Sin na da wata wayar salula, mutane kimanin miliyan 700 suna amfani da yanar gizo. Kasar Sin ta samu bunkasuwa cikin sauri, hakan ya kuma shaida cewa, hanyar musamman ta raya zaman gurguzu da kasar Sin ta zaba hanya ce mafi kyau wajen kyautata zaman rayuwar jama'a da zamanintar da zaman al'umma da farfado da zaman al'ummar Sin.(Lami)