Shugban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da muhimmin umarni game da karfafa tsarin gudanar da dokokin jam'iyya.
Shugaba Xi, wanda kuma shi ne sakataren gudanarwa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin CPC, kuma shugaban zartaswa na hukumar sojojin kasar, ya bayyana cewa, inganta dokokin jam'iyyar wani batu ne na dogon lokaci, kuma shi ne ginshikin tabbatar da nasarorin manufofin gwamnatin kasar Sin.
A cewarsa tsawon lokaci da jam'iyyar ta shafe yana nuna irin bukatar da kasar ke da ita na tabbatar da mutunta dokoki, kana kiyaye dokokin jam'iyyar zai kara ingiza cigaban manufofin gwamnatin kasar.
Xi ya bayyana cewa, ya zama wajibi jam'iyyar ta aiwatar da ka'idoji domin inganta dokokin jam'iyyar wanda ya dace da manufar babban taron jam'iyyar ta CPC karo na 18, da kuma zama na 3 da na 4, da na 5, da kuma zama 6, na kwamitin tsakiya karo na 18.
Ya kamata jam'iyyar ta rungumi tsarin sauye sauye da kirkire kirkire da kuma kafa cikakken tsarin doka bayan da aka shafe shekaru 100 da aza harsashin kafa jam'iyyar ta CPC.(Ahmad Fagam)