Xi ya fadi haka ne a yau Jumma'a da safe a yayin wani babban taron da aka shirya a nan birnin Beijing domin murnar cika shekaru 95 da kafuwar jam'iyyar kwamnis ta kasar Sin.
Mr. Xi ya kara da cewa, 'yan jam'iyyar kwaminis da jama'ar kasar Sin suna cike da imani wajen samar wa sauran kasashen duniya salon zamantakewar al'umma mafi kyau.
Bugu da kari, Xi ya yi kira da a yi kokarin amfani da tunanin Markisanci wajen kirkiro da bunkasa sabbin kirkire da ake aiwatarwa a halin yanzu a kasar Sin. Ya ce, ya kamata a dauki sabbin matakai a lokacin da ake amfani da ra'ayin Markisanci a nan kasar Sin.
Har ila, Xi Jinping, kana shugaban kasar Sin ya ce, kasar Sin ba za ta nuna karfin sojanta kan wasu kasashen duniya ba, kasar Sin tana bunkasa karfin sojanta ne domin tsaron kanta kawai. (Sanusi Chen)