Sojojin kasa da jami'an kiyaye zaman lafiya 130 da kasar Sin ta tura zuwa kasar Sudan ta Kudu a karo na karshe sun isa sansanin ayyukansu a kasar a jiya Laraba, lamarin da ya nuna cewa ya zuwa yanzu, daukacin sojoji da jami'ai 700 na kasar Sin sun riga sun isa kasar ta Sudan ta Kudu, domin gudanar da aikin kiyaye zaman lafiye. Sannan kuma, za su fara gudanar da dawainiyar MDD.
A nan gaba kadan, sojojin kiyaye zaman lafiyar na kasar Sin za su yi amfani da galibin karfinsu, wajen kafa sansani, da samun horo da MDD za ta yi musu. Bayan kammala horon za kuma su gudanar da ayyukan kare rayukan fararen hula, da ya hada da aikin sintiri da na tsaro.
An ba da labarin cewa, kafin a kammala aikin gina sansanin soja, sojojin kiyaye zaman lafiyar na Sin za su zauna ne a sansanin Tomping na MDD, da kuma babban sansanin MDD dake kasar Sudan ta Kudu.
Ban da haka kuma, an ce rundunar sojojin kasa na kiyaye zaman lafiyar ta Sin ta kunshi sojoji iri-iri, ciki hadda na kasa, da sojoji masu amfani da motocin sulke, da sojoji masu kula da yakin musamman, da masu sarrafa igwa, da masu kula da sadarwa da kuma sojojin ceto.(Lami)