in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen BRICS sun kuduri aniyar bunkasa harkokin kimiyya da fasahar kere-kere
2017-07-19 10:09:59 cri

A jiya Talata ne, ministocin kimiyya, fasahar kere-kere da kirkire-kirkire na kasashe mambobin kungiyar BRICS suka sanya hannun kan wata yarjejeniyar hadin gwiwa da nufin bunkasa harkokin kimiyya da fasahar kere-kere a tsakaninsu.

Ministan kimiyya da fasahar kere-kere na kasar Sin Wan Gang, ya bayyana yayin taro karo na biyar na ministocin kimiyya, fasahar kere-kere da kirkire-kirkire na kungiyar BRICS cewa, yarjejeniyar "Hangzhou" ta sake nanata muhimmancin hadin gwiwa tsakanin kasashen BRICS, a matsayin wani mataki na bunkasa kirkire-kirkire, tattalin arzikin duniya da samun ci gaba mai dorewa.

Shirin hadin gwiwar kungiyar ta BRICS wanda aka tsara daga shekarar 2017 zuwa 2020, ya sake jaddada muhimmancin kirkire-kirkire a matsayin ginshikin samun ci gaba mai dorewa, baya ga muhimmiyar da yake takawa a bangaren raya tattalin arziki.

Har ila shirin ya bukaci kasashe mambobin kungiyar da su zurfafa hadin gwiwa a fannin kirkire-kirkire da musayar shirye-shirye a fannin bincike, da karfafa hadin gwiwa tsakanin cibiyoyin kimiyya da musayar fasahohi.

Bugu da kari, shirin ya bukaci kasashen na BRICS da su yayata hadin gwiwar kirkire-kirkire da na masana'antu tsakanin matasa, da bullo da managartan dokoki a fannin zuba jari tsakanin kasashen kungiyar, da musayar matasa masana da 'yan kasuwa. Kana a karfafa rawar da mata ke takawa a fannonin kimiyya, fasahar kere-kere da kirkire-kirkire.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China