in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taron kasashen BRICS zai kawo sabbin damammaki ga hadin gwiwa
2016-10-13 10:55:00 cri

Taron kolin BRICS dake kunshe da kasashen Brazil, Rasha, Indiya, Sin da Afrika ta Kudu, karo na takwas da zai gudana a kasar Indiya zai baiwa mambobinsa damar tattauna batutuwa da dama, kamar kalubalolin tattalin arziki da kasashen suke fuskanta, har ma da karfafa dangantakarsu, in ji reshen Indiya na kwamitin kasuwancin BRICS a ranar Laraba.

Shugaban kwamitin, Onkar Kanwar, ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a cikin wata hira a baya bayan nan a birnin Johannesburg cewa, gungun BRICS ya gudanar da abubuwa da dama tun bayan kafuwarsa, kuma ya kasance wata babbar dama ta fuskar gina wani ginshiki daga dukkan fannoni.

Mista Kanwar ya jaddada cewa, kafa sabon bankin ci gaba da yarjejeniyar asusun ajiya da kasashen BRICS suka yi, da kuma wasu sauran shirye shirye da aka dauka a tsawon shekaru bakwai da suka gabata, suna wakiltar manyan ayyukan ci gaban da aka samu.

Taron BRICS, da zai gudana a birnin Goa na Indiya a tsakiyar watan Oktoba, zai taimaka wajen kara karfafa dangantakar tattalin arziki tsakanin kasashen gamayyar, da kokarin bai daya da kasashen mambobi suke samar domin ingiza ci gaban dorewar tattalin arziki daga dukkan fannoni da ci gaba a fadin duniya, in ji mistsa Kanwar.

Haka kuma shugabannin BRICS suna cike da fatan alheri game da taron kolin Goa mai zuwa a kasar Indiya. (Ada Maman)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China