in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babu wani shirin mai da BRICS rukunin soji, in ji jami'in Rasha
2015-05-28 10:41:14 cri

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Ryabkov a jiya Laraba ya ce, babu wani shiri na mai da kungiyar BRICS wani rukunin soji. Kungiyar musamman na kasashe ne da suka fahimci kansu suka hada ta, da kuma bukatar aiwatar da fahimtar su ta hada kai waje daya su yi aiki.

Mr Ryabkov ya yi wannan bayanin ne cikin wata hira da ya yi da kafar talabijin din Rossiya-24, ya kara da cewa, mambobin kungiyar ba su da ra'ayin siyasa ta wannan hanya. Don haka ya soki wasu kasashen yammaci da kwadayin son ci gaba da rike ragamar tattalin arzikin duniya, yana mai cewa, BRICS alama ce ta kasashen da suka yi fice a duniya, kuma kasashen yammaci ba su da yadda za su yi da wannan sabon ci gaba.

Kasashen kungiyar BRICS dai sun hada da Brazil, Rasha, Indiya, Sin da kuma Afrika ta Kudu. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China