Shugaban bankin bunkasa Afrika ADB Akinwumi Adesina, ya ce, babbar sahihiyar hanyar kawar da talauci a kasashen nahiyar Afrika ita ce ta hanyar rungumar aikin gona irin na zamani.
Adesina, ya fadi hakan ne a yayin zantawa da kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua yayin wata ziyarar aiki a kasar Ghana a farkon wannan wata, inda ya nuna cewar, bankin na ADB zai tallafa wa shirin aiwatar da aikin gona irin na zamani, ta yadda al'ummar Afrika za su iya samar da isasshen abinci da kansu.
Ya ce, idan har Afrika ta mayar da nomanta irin na zamani, to hakika za'a samar da hanyoyin samun arziki ga manoman karkara kasancewar mafi yawan su mata ne, kuma matakin zai kawo karshen shigowa da abinci daga kasashen ketare.
Adesina, ya ce, muddin ana bukatar kakkabe talauci a kasashen Afrika, to ya zama tilas a samar da hanyoyin da al'umma mazauna karkara za su samun arziki cikin gaggawa.
Sannan ya bukaci al'ummar nahiyar da su sauya tunaninsu ta hanyar rungumar sabbin dabarun noma na zamani, ta yadda za su noma su sarrafa kayan amfanin gonar ta hanyar amfani da kayayyakin masa'antun aikin gona irin na zamani.(Ahmad Fagam)