in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwararru sun yi kira ga shugabannin Afirka su kara bunkasa noma
2017-06-01 09:40:47 cri

Gungun masana a fannin noma sun ja hankalin shugabannin kasashen Afirka, da su cika alkawuran da suka dauka na ware kaso 10 bisa dari daga jimillar kasafin kudin kasashen su na shekara shekara ga bangaren raya noma. Hakan dai ita ce hanya daya tilo da ta dace nahiyar Afirka ta bi, domin fitar da miliyoyin al'ummar ta daga kangin talauci.

Masanan sun yi wannan kira ne a jiya Laraba, yayin wani taron karawa juna sani da ya gudana a kasar Uganda.

Wani rahoto da wata kungiya mai suna Oxfam mai zaman kanta ta fitar a baya bayan nan, ya nuna cewa, duk da yake kasashe da dama sun alkawarta kebe wannan adadi na kudade domin inganta noma, da yawa sun kaucewa ciki wannan alkawari, suna masu alakanta hakan ga karancin wadata. Rahoton na kungiyar Oxfam dai ya yi suka game da kamfar jari da gwamnatocin nahiyar ke sanyawa a fannin na noma.

A shekarar 2003, shugabannin nahiyar Afirka dake taro a birnin Maputo na kasar Malawi karkashin inuwar kungiyar AU, sun amince da babban tsarin inganta noma, wanda aka yiwa lakabi da CAADP, wanda zai shafi daukacin sassan nahiyar. To sai dai shekaru 10 kawo yanzu, yunwa da karancin abinci mai gina jiki, tare da kangin talauci na ci gaba da karuwa a nahiyar.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China