in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sama da mutane miliyan 5.6 ke fama da yunwa a Afrika sanadiyyar rikicin Boko Haram
2016-03-08 09:38:08 cri

Sama da mutane miliyan 5.6 ne ke fama da matsalar karancin abinci a kasashen Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi, a sakamakon rikicin kungiyar Boko Haram.

Mai magana da yawun MDD Farhan Haq, shi ne ya furta hakan a yayin taron manema labarai, inda aka rawaito jami'in kula da shirin abinci na duniya WFP yana cewa, za'a kara yawan tallafin abincin da ake samarwa daga mutane dubu 600 a shekarar da ta gabata zuwa dubu 750 ga 'yan gudun hijirar da rikicin ya tilastawa ficewa daga gidajen su, har ma da al'ummomin da suka karbi bakuncin 'yan gudun hijirar domin saukaka musu halin da suke fuskanta na rashin abinci, da matsalar karancin abinci mai gina jiki a tafkin Chadi.

WFP tana bukaci a gaggauta samar da kayayyakin domin ta samu damar gudanar da ayyukanta.

A tsakiyar watan Fabrairu ne, WFP ta kai ziyarar gani da ido a sansanonin 'yan gudun hijirar da rikicin Boko Haram a tafkin Chadi da jamhuriyar Kamaru ya tilastawa barin gidajensu, inda suke fuskantar barazanar yunwa da rashin abinci mai gina jiki.

MDD ta ce, sama da mutane dubu 100 ne rikicin Boko Haram ya tilastawa barin gidajen su a Chadi.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China