in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane miliyan 4.5 na bukatar tallafi a arewa maso gabashin Najeriya
2016-08-24 10:10:46 cri

Shirin samar da abinci na MDD WFP ya ce, yawan mutanen dake bukatar tallafin abinci a arewa maso gabashin Najeriya ya karu, zuwa mutane miliyan 4 da rabi, adadin da ya zuwa tsakiyar watan Agustar nan, ya kusan ninka wanda aka samu cikin watan Maris din da ya gabata.

Wata sanarwa da daraktan WFP mai kula da yammacin Afirka Abdou Dieng ya sanyawa hannu, ta bayyana cewa, matsalar tabarbarewar tattalin arziki, na iya kara tsananta halin da ake ciki a watan Satumbar dake tafe. Kaza lika sanarwar ta ce, akwai fargabar karin hauhawar farashin kayayyakin abinci, musamman a yankunan da suka sha fama da hare haren Boko Haram.

Wannan sanarwa dai na zuwa ne 'yan kwanaki bayan aukuwar hare haren kungiyar ta Boko Haram a wasu yankunan Najeriya da Chadi, da Cameroon da kuma janhuriyar Nijar, wanda hakan ke nuna cewa, ayyukan kungiyar na iya kara cusa al'umma cikin mawuyacin halin matsi, da kuma kamfar abinci.

Yanzu haka dai shirin WFP na kara fadada tallafin da ya ke samarwa, inda yake fatan agazawa mutane kimanin 700,000, ciki hadda samar da abinci mai gina jiki ga yara kanana su kusan 150,000 'yan kasa da shekaru 5 da haihuwa.

Har ila yau za a samar da agajin magunguna, da alluran riga kafi, da sauran kayayyakin kiwon lafiya da kungiyoyin aikin ceto ke amfani da su.

Bisa kiyasi, WFP na bukatar kudi da yawan su ya kai dalar Amurka miliyan 52, don ci gaba da ba da tallafin jin kai nan da karshen wannan shekara.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China