in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar WFP ta yi gargadin tabarbarewar yanayi a Habasha
2016-01-05 09:58:27 cri

Hukumar samar da abinci ta MDD wato WFP, ta yi gargadin tabarbarewar yanayi a kasar Habasha sakamakon fari dake addabar kasar.

Wani rahoto da ofishin na WFP ya fitar ya nuna cewa, daga farkon shekara ta 2015 ya zuwa yanzu, bukatar tallafin jin kai ta ninka har rubi uku a kasar ta Habasha, musamman a wasu yankunan da fari ya tsananta, sakamakon yanayin dumamar yanayi mai tsanani na El Nino da ake fama da shi, wanda ya haddasa karancin amfanin gona, da mutuwar dabbobin kiwo masu yawa.

Da yake karin haske game da hakan, kakakin MDD Stephane Dujarric, ya bayyana cewa, akwai kimanin mutane miliyan 10 dake bukatar tallafin jin kai a kasar, kuma hukumar WFP na da nufin agazawa gwamnatin kasar, wajen daukar nauyin a kalla mutane miliyan 7 da dubu dari shida cikin wannan shekarar ta 2016.

Mr. Dujarric ya kara da cewa, ya zuwa yanzu an tanaji kaso kusan 5% na daukacin tallafin da ake bukata a watanni 6 na farkon wannan shekara. Har wa yau hukumar ta WFP ta yi amannar cewa, gwamnatin kasar Habasha na tsara cikakken shirin da ya dace, tare da kashe makudan kudade, don dakile tasirin wannan matsala, sai dai duk da haka tana bukatar tallafi daga kasashen duniya domin cimma nasarar da ake fata.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China