in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan Tunisia: Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen inganta zaman lafiya da ci gaba a Afrika
2017-07-21 08:42:35 cri

Ministan harkokin wajen Tunisia Khemaies Jhinaoui, ya ce kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali, tare da raya tattalin arzikin kasashen Afrika.

Da yake ganawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a jiya, Khemaies Jhinaoui ya ce kasar Sin tana hadin gwiwa da kasasehen Afrika ne ta yadda za su mori juna da kuma tabbatar da daidaito ba tare da nuna fifiko ba.

Ministan wanda ke ziyarar kwanaki 5 a kasar Sin bisa gayyatar da takwaransa na kasar Wang Yi ya yi masa, ya ce a matsayin kasar Sin na mamba a kwamitin sulhu na MDD, ta kasance mai jajircewa wajen inganta zaman lafiya da sulhunta batutuwan dake daukar hankalin yankuna a siyasance.

Har ila yau, ya ce ana ci gaba da samun karin kamfanonin kasar Sin dake zuwa Afrika, al'amarin da ya ce, ya samar da karin guraben ayyukan yi tare da kawo ci gaba a wasu kasashen nahiyar.

Game da shawarar "Ziri daya da hanya daya" kuwa, Khemaies Jhinaou ya ce Tunisia na goyon bayan shawarar gina titin da ya ratsa kasashen dake cikin shawarar, kuma a shirye take ta shiga cikin ayyukan dake karkashin shirin. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China