in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Asusun ba da agaji na MDD ya baiwa Sudan dala miliyan 15
2015-10-14 09:28:16 cri

Jami'an MDD dake Sudan, sun fada a jiya Talata cewar, asusun ba da agaji na MDD ya tallafa wa kasar Sudan da kudi dalar Amurka miliyan 15.1, domin agazawa mutanen da rikici ya raba su da matsugunansu a yankin arewacin Darfur.

Ko'odinetan sashen ba da agajin gaggawa na MDD Marta Ruedas, ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa, an tanadi kudaden ne karkashin asusun ba da agaji na CERF don tallafawa mutanen dake cikin mawuyacin hali a yankin arewacin Darfur.

Sanarwar ta kara da cewa, wannan shi ne zagaye na biyu na ba da tallafin kudaden asusun na CERF na shekarar 2015, wanda za'a yi amfani da su wajen kula da rayuwar al'ummar da ke neman daukin gaggawa cikin watanni 9.( Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China