in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta kare matakin da ta dauka na korar jami'an MDD 2 daga kasar
2014-12-29 09:46:03 cri

Kasar Sudan ta sanar a ranar Lahadi cewa, ta kare matakin da ta dauka na korar wasu manyan jami'an MDD daga kasarta.

Babu abin da zai sa mu sake komawa kan wannan matakin na tusa keyar jami'an MDD biyu, kuma babu wani abin da kwamitin sulhu na MDD zai yi ganin cewa, mun yi hakan bisa tsarin kundin MDD, in ji ministan harkokin wajen kasar Sudan Ali Karti a gaban manema labarai. Matakin sallamar jami'an MDD biyu na da nasaba da 'yancin kasa da kundin MDD ya tanada, in ji mista Karti, tare da nuna cewa, gwamnatin Sudan za ta yi kokarin aiwatar da wannan mataki ga duk wani ma'aikacin MDD dake son wuce gona da iri a cikin aikinsa. Haka kuma, ministan ya kawar da wani tunanin cewa, wannan tusa keyar zai iyar kawo illa ga ayyukan ci gaba a kasar Sudan.

Babban jami'in diplomasiyyar Sudan ya yi wadannan kalamai ne bayan sakatare janar na MDD Ban Ki-moon ya yi kiran gwamnatin Sudan da ta sake dawowa kan matakin da ta dauka cikin gaggawa da kuma yin kira ga kasar da ta ba da hadin kai yadda ya kamata ga hukumomi da kungiyoyin MDD dake cikin kasar. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China