in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taron shiyya a Namibiya zai duba batun samar da ayyukan yi a Afrika
2017-02-07 09:33:11 cri

Kasar Namibiya za ta karbi bakuncin taron kungiyoyin kwadago na shiyyoyin gabashi, tsakiya, da kuma kudancin Afrika a lokacin babban taron kungiyoyin kwadago na shiyya na shekarar 2017, tsakanin 14 zuwa 15 ga wannan watan, a garin Walvis Bay, na kasar Namibiya.

Tim Parkhouse, shi ne sakatare janar na kungiyar kwadago ta kasar Namibiya, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, kimanin manyan jami'ai 40 ne za su wakilci kungiyoyin kwadago daga kasashen Kenya, Rwanda, Burundi da Madagaska kuma za su tattauna muhimmancin samar da ayyukan yi wajen bunkasa ci gaban tattalin arziki, da kuma samar da dawwamamman ci gaba.

Taken taron na bana shi ne, "Ba da horo domin samar da ci gaba da ayyukan yi, musamman ga matasa".(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China