in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar ilmin Namibiya za ta yi garambawul game da sarrafa kudade
2017-04-06 10:54:49 cri

Ma'aikatar ilmi da raya al'adu ta kasar Namibiya ta fara shirin yin gyaran fuska game da tafiyar da kudaden gudanarwarta domin samar da yanayi mai tsabta a harkar kashe kudadenta bayan da ta gamu da gibi a cikin kasafin kudinta.

Ministar ilmin kasar Katrina Hanse-Himarwa, ta sanar da hakan a lokacin da ta bayyana a gaban majalisar dokokin kasar domin kare kasafin kudin ma'aikatar.

Hanse-Himarwa, ta ce duk da irin kalubalen gibin kasafin kudi da kasar ta samu, hakan ba zai hana ta aiwatar da muhimman shirye shiryenta na ci gaban ilmi ba.

To sai dai kuma, wannan gibi zai iya shafar aiwatar da shirin bunkasa ci gaban fasahar sadarwa wato ICT a makarantun kasar, musamman wajen samar da kayayyakin aiki na ICT a makarantun ilmin kasar.

Ta ce, samar da fasahar sadarwa a makarantun kasar zai yi wuya saboda mafi yawan makarantun dake yankunan karkara ba su da lantarki, wanda kuma hakan ba zai ba su damar samun hanyoyin sadarwa ta internet ba.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China