in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Namibiya ta gabatar da dokar hana baki sayen filaye
2016-11-14 11:15:22 cri

Kasar Namibiya ta gabatar da wata dokar dake hana 'yan kasashen waje sayen filaye a cikin kasar. Dokar filaye ta shekarar 2016, wani hadin doka ce ta shekarar 1995 kan gyare gyaren filayen noman kasuwanci da doka ta shekarar 2002 kan gyare gyaren kan filayen jama'a.

A karkashin wannan doka da aka gabatar, ba za a baiwa 'yan kasashen waje damar saye ko samun filaye ba. Haka kuma ba za a ba su iznin hayar filaye ba.

A kasar Namibiya, akwai fiyalen noma fiye da dubu goma sha biyu dake wakilcin jimillar kadada miliyan 40. A cikin watan Yuni, ministan sake mayar da filaye, Utoni Nujoma, ya bayyana cewa, 'yan kasashen waje na rike da gonaki 281 a kasar Namibiya wadanda suke wakilcin kadada miliyan 1,3.

Mista Nujoma, ya gabatar da shirin doka ga majalisar dokokin kasar a karon farko a ranar Alhamis, haka kuma ya ce, wasu masu mallakar wadannan filaye ba su nan kasar ta Namibiya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China