in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rikici tsakanin mutanen wani kauye da makiyaya ya yi sanadin mutuwar mutane 33 a Nijeriya
2017-07-20 08:48:25 cri

Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta ce, a kalla mutane 33 ne suka mutu sanadiyyar rikicin da ya barke tsakanin kauyawa da makiyaya a kudancin jihar Kaduna dake arewacin Nijeriya.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Kaduna Agyole Abeh ya shaidawa manema labarai jiya cewa, yayin wasu hare-hare daban-daban guda biyu, kauyawan sun kashe makiyaya 27 mazauna yankin Kajuru, yayin da su ma wasu kauyawa 6 suka mutu.

Agyole Abeh ya ce, jami'an sa za su kama tare da gurfanar da wadanda ke da hannu wajen aikata wannan mummunan aiki a gaban kuliya.

Sai dai ya ce, zuwa yanzu, zaman lafiya ya dawo yankunan da rikicin ya shafa.

Rahotanni na cewa, sabon rikicin ya barke ne tun ranar Lahadi a lokacin da Fulani matasa suka je kauyen Ugwan Uka don daukar fansar kashe wani dan uwasu da aka yi.

Karamar hukumar Kajuru dai na da nisan kilomita 50 na tafiyar mota daga babban birnin jihar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China