A Jiya Litinin ne, aka bude bikin baje kolin fina-finan Asiya karo na farko a birnin Abuja, fadar mulkin Najeriya. Manufar bikin na kwanaki biyar wanda hukumar kula da harkokin al'adu ta Asiya ta shirya, ita ce yin cudanya tsakanin masana'antar hada fina-finai ta Najeriya mafi girma a nahiyar Afirka da takwarorinta na Asiya.
A jawabinsa yayin bude bikin, jakadan Sin dake Najeriya Zhou Pingjian, ya ce bikin wata kyakkyawar dama ce ta tallata masana'antar hada fina-finan Najeriya, wato Nollywood a nahiyar Asiya.
Jakada Zhou ya shaidawa mahalarta bikin da suka hada da ma'aikatan diflomasiya daga kasashen Asiya da na Najeriya, da masu shirya fina-finai na gida da na ketare, har ma da masu sha'awar kallon fina-finai cewa, dangantakar dake tsakanin Najeriya da Sin da hadin gwiwar Asiya da Najeriya za ta bunkasa har ma a wannan fanni.
Kasashen Asiya kimanin goma ne wadanda suka hada da Sin, Pakistan, Koriya ta kudu, Indonesia, Japan da Thailand da Vietnam, Malaysai da Phillipines da Iran suka halarci bikin.(Ibrahim)