in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen BRICS sun yi kira da tallafawa ci gaban Afrika
2015-03-19 10:46:02 cri

Kasashen kungiyar BRICS da ke kunshe da Brazil, Rasha, Indiya, Sin da Afrika ta Kudu za su mai da hankali wajen bincike da kirkirowa domin taimakawa ci gaban nahiyar Afrika yadda ya kamata, in ji wata ministar kasar Afrika ta Kudu a ranar Talata.

Ina saurin tattaunawa tare da takwarorina na wadannan kasashe domin sanya ido a fannin kimiyya da fasaha, har ma kuma da tallafawa aikin bincike da kirkirowa a matsayin muhimman abubuwan da za su taimaka da kawo ci gaban Afrika, in ji ministar kimiyya da fasaha, madam Naledi Pandor.

Madam Pandor ta yi wadannan kalamai a ranar Talata da safe kafin ta dauki hanyar zuwa kasar Brazil domin halarta taron ministocin kungiyar BRICS karo na biyu da ke gudana a ranakun 18 zuwa 19 ga watan Maris.

A yayin wannan zaman taro a Brasilia, madam Pandor da takwarorinta na sauran kasashen BRICS za su rattaba hannu kan yarjejeniyoyin huldar dangantaka ta fannin kimiyya da fasaha da kirkirowa.

Kungiyar BRICS ta kasance daya daga cikin kungiyoyi mafi kwarewa da kuma dabaru ta fuskar huldar dangantakar kasa da kasa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China