in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Lu Kang: Ya dace India ta kaucewa yin kutse domin kauracewa tada husuma
2017-07-18 19:48:01 cri

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang, ya ce ya zama wajibi kasar India, ta gaggauta kauracewa daukar matakai wadanda za su iya tada zaune tsaye, musamman a fannin kutse na jami'an soji a kan iyakar ta da Sin.

Da yake karin haske game da hakan, yayin taron manema labarai na Talatar nan, Mr. Lu Kang ya ce sojojin India, sun shiga yankunan kan iyakar Sin daga Sikkim a watan Yunin da ya shude. Kuma bayan kusan wata guda, har yanzu dakarun na India ba su janye daga yankin ba.

Lu ya ce aikin kutse na sojojin India ya jawo hankalin kasa da kasa, kuma tuni wasu jami'an diflomasiyya na kasashen ketare dake kasar Sin, sun bayyana lamarin a matsayin mai tada hankali. Jami'an sun ce batu ne mai sarkakiya, suna kuma ci gaba da tattaunawa da Sin domin kamo bakin zaren. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China