in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude banki domin tallafawa ci gaban fasahohi a Beijing
2017-07-17 12:07:39 cri

An bude wani banki a ranar Lahadi a unguwar Zhongguancun dake Beijing, wanda hakan ya kara bunkasa harkokin kasuwanci da masana'antu, don tallafawa kananan sana'o'i da fasasar zamani.

Bankin Zhongguancun, wanda ya samu amincewar hukumar gudanar da al'amurran bankuna ta kasar Sin tun a watan Disambar shekarar 2016, wasu gammayar kamfanoni 11 ne suka dauki nauyin kafa bankin a unguwar. Tuni bankin ya zuba jarin da yawansa ya kai yuan biliyan 4 kwatankwacin dala miliyan 590.

Makasudin kafa bankin shi ne domin samar da tallafin kudade ga kananan kamfanonin bunkasa harkokin kimiyya da fasaha.

Guo Hong wanda shi ne shugaban bankin ya bayyana cewa, tallafawa ci gaba kimiyya da fasaha shi ne babban burinsu.

A duk shekara sama da kamfanonin fasaha dubu 20 ne ake kafa su a Zhongguancun.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China