in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bankin duniya ya bukaci a shigar da matasa wajen raya ci gaban kasashen Afrika
2017-05-10 10:45:08 cri

Wani jami'in bankin duniya ya ce, dole ne kasashen Afrika su bullo da sabbin dabarun samar da kwarewa ga matasan nahiyar domin farfado da ci gaban biranen kasashen nahiyar.

Da yake jawabi a lokacin taron hukumar kula da muhalli ta MDD a birnin Nairobi, Mahmoud Mohieldin, babban mataimakin shugaban bankin duniyar mai kula da shirin raya ci gaban ta hanyar shigar da matasa nan da shekarar 2030 ya ce, shigar da matasa ayyukan da suka hada da na sarrafa shara, ayyukan tsaron al'umma da tsabtatacen sufuri, zai samar da inganci da ci gaban birane a fadin nahiyar ta Afrika.

Mohieldin ya ce, ya zama tilas ga gwamnatocin kasashen nahiyar ta Afrika su bullo da sabbin hanyoyi na kirkire kirkire domin inganta ayyukan hidima, da tsaro da kula da muhalli a birane.

Bankin duniyar yana karawa gwamnatocin kasashen Afrika kwarin gwiwa da su zuba jari a fannin samar da kayayyakin more rayuwa na zahiri da kuma fannin kayayyakin more rayuwa da za su kawata birane da kuma magance matsalolin talauci.

Mohieldin ya ce, aikin samar da kayayyakin more rayuwa kamar hanyoyin mota, ruwan sha da gina gidaje zai samar da karin ayyukan yi ga dubun matasa.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China