in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bankin duniya ya fidda sabon rahoto da nufin kare gurbatar muhalli a Afrika
2017-06-02 09:57:17 cri

A ranar Alhamis bankin duniya ya fitar da wani sabon rahoto da nufin inganta muhalli a biranen kasashen nahiyar Afrika wadanda ke fuskantar mummunar gurbacewa.

Rahoton mai rajin kare muhallin biranen Afrika, wanda aka fitar a Dar es Salaam, babban birnin kasar Tanzaniya ya bayyana cewar, canzawar da biranen Afrika suke samu cikin sauri yana gurbata wasu daga cikin muhallan nahiyar ta Afrika.

A cewar rahoton, kiyaye albarkatu na shuke shuke yana kara inganci da kuma kayata biranen, yana samar da damammaki na yawon shakatawa, kuma yana ba da kariya daga fuskantar matsanancin sauyin yanayi.

Rahoton ya zayyana wasu daga cikin irin halayyar da sauya biranen ke haifarwa, da suka hada da samun raguwar kudaden shiga, yawan dogaro kan tsrirrai wajen samar da makamashi, da kuma rashin ba da kyakkyawar kulawa wajen kare muhalli, musamman lalata albarkatun kasa na tsirrai, da gandun daji da albarkatun ruwa.

Rahoton ya kuma tabo wani batun dake kara zama barazana ga muhallan a biranen Afrika wato shi ne matsalar annobar ambaliyar ruwa.(Ahmd Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China