in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kenya da kasar Sin suna hadin gwiwa a kokarin gina wani yankin musamman
2017-07-17 11:06:48 cri

A kokarin da ake a halin yanzu na habaka hadin kai tsakanin bangarorin Sin da kasashen Afirka, yanzu kasar Sin da kasar Kenya suna kokarin yin hadin gwiwa domin gina wani yankin tattalin arziki na musamman a birnin Eldoret dake yammacin kasar Kenya.

Sivestre Metto, wani dan kasar Kenya, ya tsaya a kan wani filin dake birnin Eldoret, yana magana da wakilinmu cikin farin ciki, yana mai cewa: "wannan wuri zai canza sosai!"

Birnin Eldoret dake yammacin kasar Kenya, birni ne dake kan tudu. Wannan filin da aka kebe, wanda Mista Metto ya tsaya a kai, za a mai da shi wani yankin tattalin arziki na musamman, kuma shi ne irinsa na farko a kasar Kenya. Wannan yankin tattalin arziki ana kiransa da suna "yankin tattalin arziki na musamman na kogin Zhujiang". Kogin Zhujiang wani babban kogi ne a kudancin kasar Sin. Wannan sunan da aka saka wa yankin, ya sheda alakar dake tsakanin kasashen biyu fannin yankin tattalin arziki na musamman.

Wasu kamfanoni 2 ne ke daukar nauyin gina wannan yankin musamman ta fuskar tattalin arziki, wato kamfanin New South na lardin Guangdong dake kudancin kasar Sin, da kamfanin gina yankunan musamman na tattalin arziki a kasashen Afirka dake karkashin kamfanin DL na kasar Kenya. Yayin da yake bayani game da dalilin da ya sa aka saka wa yankin da za a gina a Eldoret sunan "yankin musamman na kogin Zhujiang", shugaban kamfanin New South na kasar Sin Zhu Layi, ya ce, dalilin da ya sa aka zabi wannan suna, shi ne domin kamfanin New South yana lardin Guangdong dake kudancin kasar Sin, inda babban kogi na Zhujiang ya ratsa shi. Saboda haka an yi amfani da kalmar kogin Zhujiang don nuna alamar lardin Guangdong, da hadin gwiwar dake tsakanin bangarorin Sin da Kenya.

A ranar 7 ga watan Yulin da muke ciki ne, aka kaddamar da aikin gina yankin tattalin arziki na musamman na kogin Zhujiang, inda mataimakin shugaban kasar Kenya William Ruto ya halarci bikin kaddamarwar. Bisa shirin, za a yi kokarin raya sana'o'in da suka hada da sarrafa amfanin gona, da kimiyya da fasaha na zamani, da samar da kayayyakin amfanin gida, da samar da tufafi, da na'urorin masana'antu, da aikin gine-gine a cikin yankin na musamman. Sa'an nan ana sa ran ganin kamfanonin kasar Sin da yawa su zuba jari tare da kafa ma'aikatu cikin yankin.

A jawabinsa yayin bikin kaddamar da aikin gina yankin, William Ruto, mataimakin shugaban kasar Kenya, ya ce yadda ake gina yankin musamman na kogin Zhujiang a kasar Kenya, tamkar wata ishara ce a tarihin kasar, lamarin da zai haifar da manyan sauye-sauye ga birnin Eldoret, baya ga ciyar da tattalin arzikin kasar Kenya gaba.

A nata bangare, Madam Liu Yanmei, babbar wakiliya mai kula da tattalin arziki da cinikayya ta lardin Guangdong na kasar Sin dake kasar Kenya, ta ce wannan wata dama ce da kasar Kenya ta samu na zabar yin hadin gwiwa da kasar Sin domin gina yankin musamman na tattalin arizkinta na farko, amma ban da haka kuma akwai wasu manyan dalilai. A cewarta, kasar Kenya tana da bukatar raya masana'antu, yayin da a nasu bangare, kamfanoni da yawa na kasar Sin na da bukatar fadada ayyukansu zuwa kasashen waje. Saboda haka, hadin gwiwar dake tsakanin bangarorin 2 za ta biya bukatun junansu.

A yayin da yake hira da wakilin jaridar Financial Times ta kasar Birtaniya a watan Mayun da ya gabata, Uhuru Kenyatta, shugaban kasar Kenya, ya ce yana da niyyar gayyatar karin kamfanonin kasar Sin domin su zuba jari a kasar Kenya, ta yadda za a samar da karin guraben aikin yi ga al'ummar kasar.

A nasa bangare, Willam Ruto, mataimakin shugaban kasar Kenya, ya ce matakan gyare-gyare da kasar Sin ke dauka da manufarta ta bude kofa ga kasashen waje sun sa kasar ta samu ingantattun fasahohi a fannin raya masana'antu, saboda haka yadda kamfanonin kasashen Sin da Kenya suke hadin gwiwa, zai baiwa bangaren Kenya damar koyon fasahohi da dabaru na kasar Sin, don taimakawa raya masana'antunta

Shi ma David Lagat, shugaban kamfanin DL na kasar Kenya, yana da yakini kan makomar yankin musamman na tattalin arzikin, a cewarsa, idan aka gina wannan yankin, za a samar da guraben ayyukan yi kimanin dubu 40 ga jama'ar birnin Eldoret, kuma hakan zai canza birnin har ma da kasar Kenya baki daya.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China