in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Aikin tagwayen hanyoyin da kamfanin kasar Sin ke gudanarwa ya samar da ayyukan yi ga 'yan kasar Kenya
2016-02-05 16:43:10 cri

Esther Muchai ba ta taba tunanin yin aiki a kamfanin gina titunan mota ba, kasancewarta ta girma ne a wani kauye dake tsakiyar kasar Kenya, inda ake aikin gona, kuma galibi an fi danganta wannan aiki na gine gine da maza a maimakon mata.

Matar mai 'ya'ya biyu wacce babban burinta shi ne tayi aiki a asibiti, bayan ta kammala karatu a babbar makaranta, ta samu gurbin karatu a kwalejin aikin jiyya ta gwamnati inda ta karanci fasahar gwaje gwaje.

Samun takardar shedar karatun diploma a fannin gwaje gwaje bai cika burin da Muchai ke da shi ba na yin aiki a asibiti, kasancewar bada jimawa ba matsalar rashin aikin yi da rashin kudi suka addabe ta, ala tilas tunaninta ya fara sauyawa.

Kamar dai yadda miliyoyin matasa suke yin kaura zuwa Nairobi babban birnin kasar Kenya, domin neman ayyuka yi, Muchai ta kasance bata da zabi illa yin talla domin samun kudaden biyan bukatu na gida.

Sai dai kaddara ta riga fata, cikin watanni uku da suka gabata, bayan da wani kamfanin gine gine na Sino Hydro Corporation na kasar Sin ya dauke ta aiki a matsayin lebura don aikin ginin tagwayen manyan hanyoyin mota a birnin Nairobi.

Kamfanin Sino Hydro shi ne ya yi nasarar samun kwangilar aikin fadada tagwayen hanyoyi mai tsawon kilomita 13 wadda ta hada titin Mombasa da babban titin Thika.

A watan Janairun shekarar 2015 ne shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya kaddamar da aikin gina tagwayen hanyoyin motar wanda bankin raya kasashen Afrika AFDB zai samar da kudaden gudanar da aikin, domin saukaka zirga zirga a yankunan gabashin birnin Nairobi.

Muchai ta kasance daya daga cikin daruruwan masana gwaje gwaje 'yan kasar Kenya da suka ci gajiyar aikin gina tagwayen hanyoyin, aikin da ake fata zai inganta sha'anin zirga zirga a yankuna mafiya cunkoson jama'a a gabashin birnin na Nairobi.

A yayin hira da kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua a ranar Litinin din nan, Muchai ta ce, tana alfahari da wannan dama da ta samu na zama guda daga cikin ma'aikata dake aikin samar da wannan muhimmin kayan more rayuwa a kasar.

Muchai, ta kara da cewa kwarewar da take samu a yayin gudanar da wannan aiki abu ne dake da matukar muhimmanci, sannan kuma, kudaden da ake biyan ta a kullum ya dara wanda take samu a lokacin da ta ke tallar kayan marmari

A baya tana sayar da ayaba ne ga Sinawa da kuma 'yan kasar Kenya, wadanda ke aikin ginin tagwayen hanyoyin, kafin daga bisani ta zama daya daga cikin ma'aikatan kamfanin.

Ta ce a wancan lokacin ta gamsu da yadda ma'aikata sinawa da 'yan kasar Kenya ke gudanar da ayyukansu na fadada hanyoyin motar. Daga nan ne ta yanke shawarar tuntubar jami'in dake kula da ma'aikatan domin ya dauke ta aiki, daga bisani kuma aka amince da bukatar ta

A halin yanzu tana aikin leburanci a aikin gina tagwayen hanyoyi da kamfanin ke yi, Muchai tace baya ga kudin da take samu a wannan aiki, har ila yau, tana samun kwarewa ta musamman wanda zai taimake ta a rayuwarta a nan gaba.

Muchai ta fadawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewar "Albashin mu yana da kyau matuka idan aka kwatanta da tsarin albashin kasar Kenya, kuma yanayin aikin yana da sauki. A cikin watanni uku da suka gabata, ta samu damar adana kudade masu yawa, har ma na yi niyyar fara harkokin kasuwanci"

Ta bayyana cewar wannan aikin da ta samu da kamfanin Sino Hydro Corporation na kasar Sin ya ba ta damar sauya matsuguni zuwa wani babban gida mai cikakken tsaro a wajen birnin.

Ta kara da cewar tana alfaharin kasancewa cikin matan da suka samu damar aikin gina tagwayen hanyoyi. Abu mafi muhimmanci shi ne, 'ya'yanta guda biyu zasu samu ingantacciyar rayuwa a nan gaba saboda tana iya biya musu bukatun su yadda ya kamata"

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China