in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta bude hanyar farko ta jiragen sama zuwa Afirka
2015-08-06 14:43:07 cri

A jiya Laraba ne kasar Sin ta bude hanya ta farko ta jiragen sama zuwa kasar Kenya kai tsaye, wadda ta hada birnin Guangzhou na kasar Sin da birnin Nairobi na kasar Kenya. Wannan hanya ta zamo irin ta ta farko da ta hada kasar Sin da nahiyar Afrika.

Abokiyar aikimmu Lami ta hada mana rahoto kan wannan batu.Jirage za su rika tashi sau uku a kowane mako dauke da fasinjoji daga kasar Sin zuwa kasar Kenya, a tafiyar da tsawon ta ya kai sa'o'i 11. Bayan fasinjoji sun isa birnin Nairobi, za su iya canjawa zuwa sauran jiragen sama masu isa biranen Addis Ababa, da Johannesburg, da kuma wasu sauran birane kimanin 40 na Afrika.

Kamfanin jiragen sama na Southern Airlines na kasar Sin ne ya bude wannan hanya ta jiragen sama daga birnin Guangzhou zuwa birnin Nairobi da safiyar jiya Laraba a hukunce. Bude wannan hanyar jirgin sama za ta ba da gundumawa wajen tabbatar da shirin hadin gwiwa da shugabannin Sin da na kasashen Afrika suka amincewa dangane da zirga-zirgar jiragen sama tsakanin bangarorin biyu, da kuma shirin "ziri daya da hanya daya", kuma za ta biya bukatun jama'ar kasashen Sin da na Kenya ta fannin yin mu'amala da juna. Jakadan kasar Sin dake kasar Kenya Liu Xianfa ya halarci bikin bude hanyar, ya kuma bayyana cewa, bude wannan hanya za ta inganta hadin gwiwa a tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika a fannin sufurin sama, kana za ta ingiza mu'amala da juna a tsakanin bangarorin biyu a fannonin tattalin arziki, da yawon shakatawa da kuma al'adu. Yana mai cewa,

"Bude hanyar jiragen sama da ta hada birnin Guangzhou da birnin Nairobi, za ta ba da gundumawa ga bunkasuwar hulda a tsakanin kasashen Sin da Kenya. Muna fatan zurfafa hadin gwiwa da musayar ra'ayi a tsakanin kasashen biyu ta hanyar yin amfani da wannan zarafi, domin kara amincewa da juna, da cimma moriyar juna a tsakanin kasashen Sin da Kenya."

A shekarun baya, kasar Sin da kasashen Afirka sun kara mu'amala da juna a fannin tattalin arziki, da ciniki, da kuma al'adu, kuma huldar dake tsakanin Sin da Afrika ta shiga wani sabon matsayi na bunkasuwa cikin gaggawa. Yawan fasinjojin dake zirga-zirga tsakanin bangarorin biyu na karuwa da kashi 15 cikin dari a kowace shekara, adadin da ya kai mutum miliyan 1.5.

Shugaban hukumar kula da sufurin sama ta kasar Kenya Nicolas Bodo, ya bayyana cewa, yana fatan masana'antun kasar Kenya za su yi amfani da wannan zarafi na bude hanyar jirgin sama daga kasar Sin zuwa kasar Kenyan, wajen habaka cinikayya, da hadin gwiwa, da kuma zuba jari a tsakaninsu. Ya ce,

"Ina fatan 'yan kasuwa na kasar Kenya za su yi la'akari da yadda za su ci gajiyar hulda karkashin wannan zarafi na bude hanyar jirgin sama, domin ingiza tattalin arziki a tsakanin Sin da Kenya. A sa'i daya kuma, 'yan kasuwa na tsakiyar Afrika, da gabashinta za su yi amfani da wannan hanya da kyau. Ban da haka kuma, gwamnatin Kenya za ta tsaurara matakan tsaro domin tabbatar da tsaron fasinjojin da suka fito daga kasar Sin."

A cikin shekaru biyu da suka gabata, farmakin ta'addanci ya kawo illa sosai ga sana'ar yawon shakatawa ta kasar Kenya. Kasancewar harkar yawon shakatawa daya ne daga manyan ginshikan tattalin arzikin kasar ta Kenya, don haka ake bukatar farfado da ita cikin gaggawa.

Shugaban kwamitin yawon shakatawa na kasar Kenya Mureithi Ndegwa, ya bayyana fatan samun karin Sinawa da za su rika zuwa Kenya domin yawon shakatawa sakamakon bude wannan hanya ta jiragen sama. Ya kuma kara da cewa,

"Ko shakka babu, bude wannan hanya zai kawo karin masu yawon shakatawa daga kasar Sin. Mun dora muhimmanci sosai kan kasar Sin, kuma muna daukar jerin matakai na jawo karin masu yawon shakatawa daga kasar ta Sin."

Fasinjoji za su rika tashi sau uku a ko wane mako zuwa birnin Nairobi daga birnin Guangzhou, tafiyar da tsayon ta ya kai sa'o'i 11. Yanzu haka kuma, an bada farashi mai rangwame wajen wannan hanya, inda farashin tikiti na karamar kujera zuwa da dawowa bai wuce kudin Sin Yuan 4900 ba. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China