in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin kasar Sin ta baiwa 'yan gudun hijirar dake Kenya agaji
2017-06-09 13:16:53 cri

A ranar Larabar da ta wuce ne, aka yi bikin mika kayan agajin abincin da gwamnatin kasar Sin ta baiwa 'yan gudun hijira a cikin wata unguwar 'yan gudun hijira mai suna Kakuma dake samun mafaka a kasar Kenya.

An kafa mafakar 'yan gudun hijira ta Kakuma a yankin arewa maso yammacin kasar Kenya, kusa da kan iyakar kasar da Sudan ta Kudu, a shekarar 1992, wadda ta kasance daya daga cikin sansanonin 'yan gudun hijira mafi girma a duniya. Ya zuwa watan Fabrairun bana, 'yan gudun hijira fiye da dubu 164 da dari 5 ne suka yi rajista a mafakar, wadanda suka zo daga kasashe kimanin 18, da suka hada da Sudan ta Kudu, da Somaliya, da Burundi, da Habasha, da Kongo Kinshasa, da dai sauransu.

A yayin bikin mika kayan agajin da ya gudana a ranar Laraba, 'yan gudun hijirar sun yi layi don jiran samun tallafin abinci da suka hada da masara da dawa. Lokacin da wani daga cikinsu ya hangi fuskar Sinawa da suka kai abinci wajen, ya yi murna matuka, har ma ya yi tafi yana mai cewa,

"Sunana Congonso, na zo daga Habasha ne. Yau shekaruna 25, kuma na zo nan ne shekaru 4 da suka wuce. Kun zo Kakuma domin kula da mu, don haka muna farin ciki kwarai."

Wani dan gudun hijira mai suna Mabior daga kasar Sudan ta Kudu, kuma ya yi shekaru 7 yana zaune a Kakuma. Bayan da ya samu agajin abincin da kasar Sin ta bayar, ya ce,

"Yadda aka taimake mu yana da kyau, kuma muna godiya kwarai da gaske, kan tallafin da kasar Sin ta ba mu. Kalamai ba su iya nuna godiyata ba. Ina fatan za a ci gaba da ba mu taimako."

A watan Mayun bana ne, gwamnatin kasar Sin ta baiwa hukumar samar abinci ta duniya da agajin da ya hada da masara da dawa, wadanda nauyinsu ya kai ton dubu 9, kuma darajarsu ta kai dalar Amurka miliyan 5, Domin kai dauki ga 'yan gudun hijira dake wasu kasashen Afirka fiye da dubu 100, wadanda suke zaune cikin manyan sansanonin 'yan gudun hijira na Dadaab da Kakuma dake kasar Kenya. Sa'an nan abincin da aka mika wa 'yan gudun hijirar a wannan karo wani bangare ne na dukkan agajin da kasar Sin ta baiwa hukumar samar da abinci ta duniya.

Jakadan kasar Sin a Kenya, mista Liu Xianfa, wanda ya halarci bikin mika kayan agajin kana ya mika da hannunsa, ya gaya ma manema labaru cewa,

"A wannan karo, kasar Sin ta samar da taimako ga wasu kasashen dake gabashin Afirka, da suka hada da Kenya, Sudan ta Kudu, da Somaliya. Hakan ya nuna tausayi da kaunar da gwamnatin kasar Sin da jama'arta suka nuna ma 'yan gudun hijira, da jama'ar kasashen gabashin Afirka, wadanda ke fama da fari. Nan gaba za mu ci gaba da taimakawa jama'ar dake gabashin Afirka ta hanyoyi daban daban, don kyautata zaman rayuwarsu."

A nata bangare, Annalisa Conte, wakiliyar musamman ta hukumar samar da abinci ta duniya, ta nuna godiya ga gwamnatin kasar Sin, inda ta ce,

"Agajin da gwamnatin kasar Sin ta bayar yana da amfani sosai. Saboda wadannan 'yan gudun hijira ba su da sauran hanyoyin samun abinci, illa dai tallafin da hukumar samar da abinci ta duniya ke bayarwa. Don haka, bisa wadannan agajin, za mu ci gaba da samar musu da abinci a kowane wata, ta yadda dukkan 'yan gudun hijira fiye da dubu 100 dake zaune da sansanin Kakuma za su amfana."

A shekarar da muke ciki, kasashen dake gabashin Afirka da yawa suna fama da radadin bala'in fari mai tsanani. Bisa la'akari da mawuyacin halin da suke ciki ne, ya sa kasar Sin ta ba da agaji cikin gaggawa. Ban da abinci da aka mika ma 'yan gudun hijira dake Kenya a wannan karo, kasar Sin ta samar da karin agajin abinci da yawa ga kasashen Sudan ta Kudu, da kuma Somaliya.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China