Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya bukaci da a kara inganta ilimin kiwon lafiya, domin baiwa al'ummar Sinawa damar cin gajiyar rayuwa mai cike da koshin lafiya.
Mr. Li Keqiang ya ja hankalin masana a fannonin ilimi da lafiya, tare da sauran masu ruwa da tsaki, da su bada gudummawar samar da managartan sauye-sauye, ta yadda za a inganta harkokin kiwon lafiya a fadin kasar Sin.
Li Keqiang wanda ya bayyana hakan yayin wani taro na masu ruwa da tsaki game da sha'anin kiwon lafiya da ya gudana a jiya Litinin, ya ce akwai bukatar daukar darasi daga sauran kasashe da suka samu ci gaba a wannan fanni, tare da sanya magungunan gargajiya da na zamani a mizani guda, a kuma horas da karin kwararru wadanda za su tallafawa wannan aiki.
Ita ma mataimakiyar firaministan kasar ta Sin Liu Yandong, ta jaddada wannan bukata ta Mr. Li, tana mai cewa biyan bukatun al'umma, da bunkasa tsarin ilmantarwa a fannin kiwon lafiya, da na bada hidima a bangaren, su ne hanyoyin da za su bada damar samar da kwararru da ake bukata.(Saminu Alhassan)