in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
FAO ta bukaci a sauya matakan kawo karshen yunwa a kahon Afrika
2017-07-14 10:12:52 cri
Hukumar samar da abinci da kula da ayyukan gona ta MDD FAO, ta yi kira ga kasashen yankin kahon Afrika, su yi wa dabarun ayyukan gona garambawul tare da kara kaimi wajen kula da sauyin yanayi don samar da wadataccen abinci.

Wakilin Hukumar FAO a Kenya Gabriel Rugalema, ya ce ingantattun dabaru da kara zuba kudi da amfanin da fasahohin zamani su ake bukata wajen bunkasa samar da abinci a kahon Afrika a lokcin da ake tsaka da fama da matsanancin yanayi.

Gabriel Rugalema na wannan jawabi ne yayin taro kan kawo karshen yunwa a yankin kahon Afrika, wanda ya samu halartar wakilan Gwamnatoci da na hukumomi da kuma masana.

A rahotonsa na baya-bayan nan, Ofishin MDD mai kula da ayyukan jin kai, ya yi kiyasin cewa mutane miliyan 26 ne ke fama da yunwa a yankin kahon Afrika.

Wakilin na FAO ya ce matsalar yanayi da dabarun ayyukan gona na dauri da rashin mai da hankali wajen tunkarar matsalar yanayi, su ne ke kawo tsaiko ga yunkurin ciyar da jama'a dake kara karuwa a yankin.

Ya kara da cewa, zamanantar da ayyukan gona tare da inganta muhimman abubuwa da suka hada da adanawa da rarrabawa da kuma sayar da amafanin gona, su ne jigo wajen kawo karshen yunwa a yankin.(Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China