in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Akwai bambanci tsakanin keta iyakar kasa da India ta yi a yanzu da na da
2017-07-13 11:00:32 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya ce, sojojin tsaron kasar India sun shiga yankin kasar Sin ba bisa doka ba, ta hanyar keta iyakar Sikkim dake tsakanin kasashen biyu, kuma akwai bambanci sosai a tsakanin irin sabani da aka samu a tsakanin sojojin tsaron kasashen biyu a da da na wannan karo.

Kakakin ya bayyana haka ne a yayin taron manema labaru da aka saba yi a jiya Alhamis a nan birnin Beijing. Ya ce wasu rahotanni sun bayyana yadda sakataren harkokin wajen kasar India S. Jaishankar, wanda ya taba zama jakadan farko na kasar a kasar Sin, na nuna ra'ayinsa kan dauki ba dadi a tsakanin sojojin kasashen biyu, a yayin jawabinsa a Singapore. An ce Mr. Jaishankar ya bayyana cewa ba za a bari irin wannan dauki ba dadi a kan iyaka ya kawo illa ta dindindin tsakanin kasashen biyu ba.

Game da hakan, Mr. Geng ya bayyana cewa, akwai wasu abubuwan na musamman game da tarihin kan iyarkar Sikkim, wato a cewar sa iyaka ce daya tak da aka shata tsakanin kasashen Sin da India, saboda haka take da bambanci da iyakokin dake gabas, da na tsakiya da kuma yamma. Mr. Geng ya kara da bayyana bukatar bangaren India da ya janye sojojinsa daga yankin Sin ba tare da sharadi ba, kana a gaggauta warware wannan batu yadda ya kamata. (Bilkisu)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China