in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta fidda tsarin shawo kan cututtuka masu dadewa
2017-02-14 19:50:09 cri
Hukumar zartaswar kasar Sin, ta wallafa tsarin musamman mai kunshe da kudurori da ake fatan cimmawa, a matsakaici da kuma dogon zango, wajen shawo kan cututtukan dake da wahalar magani.

Rahotanni sun bayyana cewa tsarin na shekaru 10, ya kunshi shirin kasar na kariya, tare da magance cututtukan da ke da wahalar magani, ko masu dadewa ana faman jiyyar su, kamar ciwon daji, da na zuciya da Sukari da dai sauran su.

Tsarin wanda aka fitar a Talatar nan, zai maida hankali ne ga kyautata lafiyar al'umma, da rage yiwuwar kamuwa da wadannan nau'o'i na cututtuka tsakanin al'ummun dake cikin hadarin kamuwa da su, tare da daukar matakan inganta lafiyar wadanda suka riga suka kamu da su.

Har wa yau tsarin na kunshe da wasu muhimman sassan 8, da suka kunshi sashen ilmantarwa, da inganta matsayin gwaji da jinya, da inshorar lafiya da ma dabarun bada tallafi ga majiyyata. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China