in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya gudanar da muhimmiyar ziyara a birnin Mogadishu
2014-10-30 09:49:45 cri

A jiya Laraba ne babban magatakardar MDD Ban Ki-moon ya isa birnin Mogadishun kasar Somaliya, a wani mataki da ake kallo a matsayin muhimmi ga yunkurin dora kasar kan sahihiyar hanyar ci gaba.

Rahotanni sun ce, Mr. Ban ya isa birnin na Mogadishu ne tare da tawagar kusoshin babban bankin duniya da na bankin IDB.

Tawagar wadda ta kunshi jagoran bankin duniya Jim Yong Kim, da shugaban bankin IDB Ahmed Mohamed Ali ta kuma gana da wakilan gwamnatin kasar, ciki hadda shugaba Hassan Sheikh Mohamud, da firaminista Abdiweli Sheikh Ahmed, da kuma kakakin majalissar dokokin kasar Mohamed Osman Jawri.

Yayin taron, Mr. Ban ya alkawarta ci gaba da baiwa kasar ta Somaliya tallafin da ya dace a fagen karfafa tsaro, da wanzar da ci gaba, da kuma dorewar mulkin dimokaradiyya. Ban ya kara da cewa, Somaliya na kan turba ta gari, yana kuma da imanin al'ummarta za su kai ga cimma nasarar magance kalubalen dake fuskantar kasar ta su.

Daga nan sai ya yi kira ga jagororin kasar da su hada gwiwa da sauran kasashen duniya, wajen ganin an sanya daukacin al'ummun kasar, ciki hadda wadanda ba a dama wa da su cikin sha'anin sake ginin kasar, da ma na wanzar da zaman lafiya.

Shi kuwa a nasa jawabi, shugaba Hassan Sheikh Mohamud godewa tawagar ya yi bisa abin da ya kira muhimmiyar gudummawa da suke baiwa yunkurin daidaita al'amura a kasarsa, dama sauran yankuna da sassan duniya baki daya. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China