Dakarun dake samun goyon bayan MDD a Libya, sun soki sakin dan tsohon shugaban kasar Saif Al-Islam Gaddafi. Dakarun sun ce, an shirya taron neman sulhunta sassan kasar karkashin hukumar dake da alhakin hakan a ranar Lahadi a Zintan, kuma a ra'ayin wakilan dakarun, sakin Saif Al-Islam Gaddafi ya sabawa doka, kuma cin amanar dubban wadanda suka rasa rayukan su ne, sakamakon kisan masu zanga zanga da shi Saif Al-Islam din ke da hannu a aikatawa.
Dakarun sun ce, za su yi bincike game da sakin Saif Al-Islam.
Rahotanni dai sun bayyana cewa, wasu dakaru da ke tsare da Saif Al-Islam Gaddafi ne suka sake shi a ranar Asabar din karshen mako, daga gidan yarin birnin Zintan, mai nisan kilomita 180 kudu maso gabashin birnin Tripoli.(Saminu)