in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta samar da dokar daidaito ta bai daya ga kamfanoni cikin gida da na ketare
2017-07-06 10:28:07 cri

Gwamnatin kasar Sin za ta inganta dokokin da za su samar da kyakkyawan yanayin yin rijistar ba tare da nuna banbanci ba ga kamfanonin cikin gida da na kasashen waje dake da muradin kafa masana'antunsu a cikin kasar.

Idan aka tabbatar da wannan shirin, kasar Sin za ta kara samar da dokoki da tsare tsare wadanda za su karfafa harkokin cinikayya, kamar yadda gwamnatin Sin ta ayyana bayan kammala zaman majalisar gudanarwar kasar, wanda firaiminista Li Keqiang ya jagoranta.

Sanarwar tace wannan yunkuri zai kara samar da tsabta a sha'anin zuba jarin kamfanoni masu zaman kansu kuma zai kara janyo hankali masu zuba jari a kasar daga kasashen ketare.

Kasar Sin za ta yi amfani da dukkan sahihan hanyoyi da suka dace wajen janyo hankalin masu zuba jari ta hanyar hadin gwiwar gwamnati da hukumomi masu zaman kansu domin zuba jari a sabbin ababen more rayuwa don amfanin al'umma.

Gwamnati za ta samar da hannayen jari da nufin amfanin al'umma, da ayyukan samar da ababen more rayuwa don tallafawa shirin nan na ingancin kayan da kasar Sin ke kerawa nan da shekara ta 2025 wato "Made in China 2025" plan.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China