in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta fitar da takardar kare ikon mallakar dukiya karo na farko
2016-11-28 11:00:31 cri

Jiya Lahadi a hukunce kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da majalisar gudanarwar kasar Sin suka fitar da wata takarda game da ra'ayinsu kan batun yadda za a kare ikon mallakar dukiyar al'ummar kasar, da kuma kara kyautata manufar kare ikon yan haka din. Wannan ne karo na farko da gwamnatin kasar Sin ta fitar da irin wannan takarda bisa sunan kwamitin tsakiya na JKS.

Abu mafi muhimmanci yayin da ake kokarin kare ikon mallakar dukiyar al'ummar kasar shi ne tafiyar da harkokin kasa bisa doka, takardar tana kumshe da abubuwa a fannoni biyar, tare kuma da tanadar ayyuka a fannoni goma da suke da nasaba da kara ba da kariya ga ikon mallakar dukiya, da kyautata dokokin ba da kariya ga dukiya, da warware sabane-sabane kan ikon mallakar dukiya da ba a daidaita ba a tarihi, da kyautata tsarin cika alkawari na hukumomin gwamnatin kasar, da kyautata tsarin dukiya a kasar, da kara ba da kariya ga ikon mallakar fasaha, da kago wani muhalli mai inganci domin kyautata aikin kare ikon mallakar dukiya a kasar da dai sauransu.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China