A yau ne majalisar wakilan jama'ar kasar Sin kana babbar hukumar da ke kafa doka a kasar ta kira taro, inda aka zartas da sabuwar dokar tsaron kasa. Sannan nan shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ba da umurnin fara amfani da doka kamar yadda doka mai lamba 29 ta tanada.
Abubuwan da ke kunshe cikin dokar sun hada da ayyukan tsaron kasa a fannoni 11, kamar su siyasa, yankunan kasa, aikin soja, al'adu, kimiyya da fasaha. Kuma dokar ta fara aiki daga yau.(Kande Gao)