in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar wakilan Najeriya za ta binciki tsohon shugaban kasar bisa zargin badakalar mai
2017-07-06 09:26:44 cri

A ranar Laraba majalisar wakilan Najeriya ta ayyana cewar, za ta binciki tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan bisa zarginsa da hannu kan badakalar albarkatun man fetur na kasar.

A wata sanarwa da shugaban majalisar wakilan kasar ya fitar ya nuna cewa, majalisar tana sa ran Jonathan zai amsa tambayoyi game da bincike kan yarjejeniyar cinikin rijiyar man fetur din kasar da aka fi sani da Malabu.

Akwai takaddama mai yawa game da batun dala biliyan 1.3 na kudaden cinikin rijiyar man kasar ta "OPL 245" mafi daraja. An yi ittifakin rijiyar man ita ce mafi daraja a yammacin Afrika.

An kiyarsata rijiyar man na da gangar danyen mai da yawansa ya kai ganga biliyan 9, kuma an sayar da ita ne ga kamfanonin hakar mai na Shell da ENI a kan tsabar kudi dala biliyan 1.3 a shekarar 2011, a lokacin da Jonathan ke shugabancin kasar.

Sai dai kuma, ana zargin an kasafta kudaden ne tsakanin manyan kusoshin gwamnatin kasar a wancan lokacin a matsayin cin hanci, inda gwamnatin kasar ta amfana da dala miliyan 210 kacal daga cikin makudan kudaden cinikin rijiyar man ta OPL 245.

Jonathan da sauran jami'an gwamnatin Najeriya, ciki har da tsohon antoni janar na kasar Mohammed Bello Adoke, da tsohuwar ministar man fetur ta kasar Diezani Alison-Madueke, suna daga cikin wadanda ake zargin sun karbi cin hanci na kudaden cinikin rijiyar man.

Sai dai tsohon shugaban na Najeriya ya sha nesata kansa cikin wannan badakala, yana mai cewa, wasu mutane ne ke yunkurin zubar masa kima a idon duniya.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China