in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana sa ran bude taron kolin AU karo na 29 a Addis Ababa a yau Talata
2017-06-27 09:45:38 cri

A yau Talata ake sa ran bude taron koli na kungiyar tarayyar Afrika karo na 29 a helkwatar kungiyar ta AU dake Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha.

Za a gudanar da taron kolin karo na 29 ne daga ranar 27 ga watan Yuni zuwa 4 ga watan Yuli, taken taron na wannan karo shi ne "Tabbatar da hadin kan yankuna ta hanyar amfani da matasa a matsayin jari."

Cikin wata sanarwa da kungiyar kasashen Afrikan ta fitar a ranar Litinin ta nuna cewa, za'a gudanar da taron kwamitin wakilai na din din din (PRC) karo na 34, a kwanaki biyun farko na taron kolin wato tsakanin 27 da 28 ga watan Yuni.

Ana sa ran taron na PRC ne zai shirya ajandar taron kolin na AU inda za'a gabatar da shawarwari mafiya dacewa wanda za'a gabatarwa majalisar kolin domin neman amincewarta, wanda ake sa ran za'a gudanar daga ranar 30 ga watan Yuni zuwa 1 ga watan Yuli.

Hukumar gudanarwar AU ta sanar cewa, taron na kwamitin wakilan din din din zai kunshi dukkan jakadu 55 na kasashen mambobin kungiyar wadanda ke zaune a Addis Ababa da kuma sauran muhimman jami'an na AU.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China