in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
IS ta harbo jirgi mai saukar ungulu a Syria
2017-07-03 12:55:06 cri

Kungiyar IS ta harbo wani jirgi mai saukar ungulu a Syria wanda ke dauke da kayan abincin da ya nufi birnin Deir al-Zour a gabashin Syria a ranar Lahadi, lamarin da ya haddasa hasarar rayuka wanda kawo yanzu ba'a kammala tantancewa ba, kamar yadda tashar talabijin ta kasar ta ba da rahoto.

An harbo wannan jirgin ne kuma aka cinna masa wuta a lokacin da yake kokarin raba kayan tallafin abinci da sauran kayayyakin bukatun rayuwar yau da kullum a yankin birnin Deir al-Zour, wanda ke hannun mayakan IS.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China